Ita dai wannan hanya itace ta hada karamar hukumar Yorro da wasu sassan jihar Adamawa, wadda yanzu haka matafiya suka kaurace mata sakamakon lalacewar da hanyar ta yi fiye da shekaru goma.
Hanyar Yorron mai tazarar kilomita 20 na daga cikin manyan hanyoyi a jihar Taraba da suka dade da lalacewa, lamarin da ya maida yankin baya duk kuwa da albarkatun noma da ma’adanan dake yankin.
To sai dai gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Isiyaku ya ce yanzu gwamnatin jihar ta bayar da aikin hanyar akan kudi sama da Naira Biliyan Biyar, batun da wasu ke ganin akwai abin dubawa kan yadda aka bada aikin, da kuma kamfanin da zai gudanar da aikin hanyar.
Karamar hukumar Yorro dake zama cibiyar ‘yan kabilar Mummuye. Mai martaba sarkin Mummuye Alhaji Ado Adamu Mazang, ya bayyana farin cikinsa kan wannan aiki, inda yake cewa al’ummar yankin zasu ci moriyar wannan aiki.
Gudanar da wannan aiki na hanyar Yorro zai taimaka wajen bunkasa harkar noma wanda zai habaka tattalin arziki a yankin da kuma jihar baki daya.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5