A shirin mu na mata, a yau kuwa mun waiwayi wannan al’adar ta Mata ta ajiye samari da dama domin biya musu bukatunsu na yau da kullum.
Akan haka ne ma muka samu zantawa da wasu 'yan Mata, kowacce da ra’ayoyinta da kuma dalilanta na tara Samari da yawa.
Daga ciki wasun su na da ra’ayin cewar;
“ a halin da ake ciki ba a zama da saurayi a cewar wata ko a yanzu tana da Samari ta guda biyar, daya na sayan waya ne, daya mai saka kudi a waya, daya mai yin anko, dayan kuwa matsolo ne. Sai na karshen shine na gasken wanda zata aura , ta ce ta na ajiye su ne domin rage wasu abubuwan more rayuwa kuma kowannen na tunanin shi za a aura.
Wata kuwa cewa ta yi ‘ba za ta iya zama da saurayi daya domin da zarar sun san su kadai aka ajiye sai su fara yanga.
Wata kuwa cewa ta yi ita ba ta da ra’ayin ajiye samari da yawa domin a cewar ta hakan ba da’a ba ce.
Kowacce dai da ra’ayinsa ta na ajiye samari akalla hudu domin guda daya ba zai iya dauke duka nauyin bukatun budurwa ba, daya ana ajeye shi ne don harkar anko daya na kudi, saboda idan ba’ayi wa Samarin haka harka bata tafiya kuma dukkansu ana yi musu karyar za'a aure su.