Likitocin fata, sun bayyanar da wasu abubuwa da ke da matukar muhimanci ga mutane, wajen tattalin lafiyar fatar jiki. Musamman ta fuska.
A wani bincike da suka gudanar da ke bayyanar, da manya-manyan dalilan da ke sa fuskoki ko fatar jiki kan tsofe bayan shekaru basu jaba.
A banganren mata, sau da yawa mata kanyi amfani da wasu man shafe-shafe, wadannda basu da masaniyar sinadaran da akayi amfani da su, wajen hada wannan man. Mata har ma da maza na da kyashin share fuskokin su sau biyu a rana, wanda wannan na taimakawa kwarai wajen kare fata da ga wasu cututtuka.
Sun kara da cewar, da kace mutane zasu dauki wasu kalolin mai, don shafama jiki a kowane lokaci. Kuma su guji canje-canjen mai a kowane lokaci, kawai su zauna ma kalan mai daya ko biyu, lallai wannan zai taimaka ma lafiyar fata.
Wani abu da mafi akasarin mutane kanyi musamman ma matasa shine, su kan dinga shafar fuska a kowane lokaci, ko kuma su dinga kokarin fasa kuraje da suke fito musu a fuskokin su, wannan na tai makawa matuka, wajen saka fata cikin hatsari.
Abu mai matukar muhimmanci shine, mutane su guji wanke fuska da yawa, ko kuma ace su dinga wanke fuska sannu a hankali.
Akwai matukar bukatar mutane su daina, amfani da kowane irin kayan kwalliya a fuskokin su, domin kuwa daga neman giba akan iya samo rama.