Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace ana sa ran za a gayyaci Iran wajen wasu muhimman taro game da makomar siyasar kasar Syria wanda za a yi wannan makon a Vienna.
A lokacin taron mai zuwa a ranakun Alhamis da Juma’a, Amurka da sauran kasashen duniya masu fada a ji, zasu tattauna akan abinda kakakin ma’aikatar John Kirby ya kira wani matakin siyasa mai sarkakiya.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ne zai jagoranci tawagar Amurka. Haka kuma halartar Iran zai zama wani matakin zakudawa gaba game tsakaninta da Amurka da kasashen duniya masu fada aji.
Musamman idan aka yi la’akari da yadda manyan kasashen duniyar ke kaucewa tsoma Iran a lamura in an dauke maganar yarjejeniyar da aka cimma ta Nukiliyar Iran a watan Yulin da ya gabata.