Tana Sayar Da Jakkuna Da Takalman Duwatsu

Takalman Duwatsu

Yayinda ya rage saura kwanaki kadan a yi bukin sallah, yanzu ne lokacin da kofar 'yan kasuwa ke budewa saboda shirye-shiryen sallah.

Malama Hafsa, wadda aka fi sani da Maman Hanifa ta fito da wasu takalma da jakkuna sabon yayi.

A wata hira da Baraka Bashir wakiliyar dandalin VOA, Malama Hafsa tace tana saida kayan yara da takalma, amma tace tafi ciniki dab da Sallah don lokacin aka fi sayayya. Ta kara da cewa a lokacin ne kuma jama'a, ke son sayen kaya musamman ma wadanda ake yayi yayinda kuma ake murnar kammala azumin watan Ramadan.

Akwai wasu takalma da jakkuna har ma da sarka masu duwatsu da Malama Hafsa ke saidawa. Tace daga Ghana ake kawo mata su kuma cikin kwanaki uku kachal har ta sayarda guda goma shabiyu, don sabbin yayi ne, a Ghana kawai ake yin su sai kuma wajenta don ana kai su kasashen waje.

Malama Hafsa ta ce an bincika mata Lagos ko akwai irin kayan amma ba a samu ba, don a Lagos ake fara samun kayan yayi kafin su bazu wurare dabam da bam. Ta kuma ce kayan na samun karbuwa sosai saboda yadda mata (iyaye da 'yan mata) ke sha'awar kayan kyale-kyale, don kowacce mace na so a fara ganinta da su.

Malama Hafsa dai tace wadannan kayayyakin su kan kai naira dubu uku. Ta kuma janyo hankalin mata tare da yi masu huduba akan su rungumi sana'a kada su zauna haka nan.
Ga Baraka Bashir da hirar da suka yi.