Duk da cece kucen da ya taso dangane da zargin da akayi wa shugaban ‘yan wasan Super Eagles Stephen Keshi akan neman kwantaragi da kasar Cote d’Ivore, shugaban bai yi kasa a gwiwa ba wajan mika tsarin shirin da yayi domin shirya ‘yan wasan sa na Super Egles ta yadda za su fuskanci ‘yan wasan kasar Tunisiya a gasar shiga cin kofin Afirka da za’a buga a shekarar 2017.
Majiya ta musamman daga hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta fada wa mujallar complete Sport cewar, babban shugaban ya aika da tsarin shirin wasan nasa ne da ya yi wa lakabi da “yadda zamu doke Tanzaniya.”
Kamitin fasahar kwallon kafa ke da alhakin amincewa da wannan tsari.
Idan an amince da tsarin , za a bude zangon wasan wanda za’a yi wa mazauni a Abuja kafin sauran abokan wasan na su da ke zama a kasashen waje su iso kwanaki kadan kafin su kama hanya zuwa Tanzaniya.
Keshin ya mika rahotan sa na karawar su ta farko da kasar Chadi a Kaduna, inda wasan ya tashi 2 – 0.
Wani mamba na kwamitin ya misalta rahoton a matsayin mai saukin ganewa kuma a kan lokaci.