Wannan na zuwa ne yayin da yan gudun hijiran da aka kwato yankunansu ke neman da a maida su garuruwansu. Su dai wadannan ‘yan gudun hijirar da yanzu suka rage a sansanonin da aka tanadar, na yabawa da irin kulawar da sukace hukumomi na yi musu a yanzu. To amma sun bakaci a mayar da su gida tunda hankula sun fara kwantawa.
Hukumomin bada agaji sunce yanzu haka akwai shirye shiryen da akeyi na ganin an tallafa tare da sake tsugunnar da al’umomin dake komawa. Jami’in hukumar kula da agajin gaggawa ta NEMA mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, Alhaji Sa’adu Bello, ya bayyana irin matakan da ake ‘dauka.
Yanzu haka ma kwamitin sake farfado da yankunan da aka lalata dake karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro Janaral TY Dan Juma, da kuma hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dan Gote, sunce muddin ana son sake tsugunnar da mutanen da lamarin ya shafa, to tabbas za a kashe kudi kusan Naira Trillion biyu, wanda haka ne nunin akwai jan aiki gaban mai gona.
Your browser doesn’t support HTML5