Kungiyar Taliban ta fito karara ta ce duk wata yarjajjeniyar zaman lafiya tsakaninta da gwamnatin kasar, za ta zama tamkar mika wuya ce ga abin da ta kira, "abokan gaba" kuma hakan ya saba ma Musulunci.
WASHINGTON D.C —
Kungiyar gwagwarmayar ta raba ma manema labarai bayanan nata, ciki har da Muryar Amurka, a matsayin martanin rahoton da ke nuna cewa wasu wakilanta wata tsohuwar kungiyar gwagwarmaya cewa a shirin ita Taliban din ta ke higa tattaunawar zaman lafiya da gwamnati.
Wannan sanarwar da kuma labarin cewa Amurka, na shirin tura karin sojojinta zuwa Afghanistan, don su taimaki sojojin gwamnati su yi galaba kan Taliban, ya kara jaddada damuwar da tuni ta wanzu kan yiwuwar kara faskara da zubar jini za ta yi a wannan shekarar.