Amurka na barazanar kakaba takunkumin nan take don hana Rasha da kuma duk wani dake kokarin yin shishshigi yanzu ko kuma nan gaba a zabubbukan Amurka.
Shugaba Trump, ya ayyana wannan shiri ne a wani zaman gaggawa da aka gudanar jiya Laraba, lokacin da ya sanya hannu a kan wata dokar shugaban kasa da ta bada izinin aza takunkumin tattalin arziki da wasu hukunce hukunce kan duk wani mutum ko kungiya ko kuma kasa da ta tsoma hannu a cikin zaben tsakiyar shekara da za’ayi a ranar 6 ga watan Nuwamba.
An zartar da wannan doka makonni takwas kafin masu zabe su kada kuri’a da kuma kare hare hare kan shirye shiryen zaben Amurka, wanda ya hada da Injinan zabe, da kuma bayanan masu zabe, kutse akan 'yan takara ko kuma jam’iyyun siyasa gami da kamfe da bayanai marasa inganci.