Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana mutuwar Flying Officer Tolulope Arotule, mace ta farko da ke sarrafa jirgin yaki a tarihin Najeriya a matsayin wani babban rashi bayan wani hadarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwarta a sansanin mayakan da ke jihar Kaduna.
Marigayiyar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Ijanmu ce da ke jihar Kogi, an haifeta ne a birnin Kaduna ranar 13/12/1995. Ta fara karatun firamare a makarantar yaran sojojin sama da ke jihar Kaduna a shekara ta 2000 zuwa 2005, daga nan ta wuce zuwa makarantar sakandaren yaran sojojin sama duk dai a jihar a shekara ta 2006, inda ta kammala a shekara ta 2011 kafin daga bisani ta wuce zuwa makarantar horas da hafsoshin soja a shekara ta 2012.
Arotule ta zama mace ta farko da ke sarrafa jirgin saman yaki a shekara ta 2017 kana aka kaddamar da ita a shekara ta 2019 a matsayin cikakkiyar mai tuka jirgin yaki bayan kwasa-kwasan da ta yi a kasashen Afirka ta Kudu da Italiya.
Ita ce ta gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari da sabon jirgin yakinnan mai suna “109 Power Attack Helicopter” a yayin kaddamar da shi a dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar 6 ga watan Fabrairun 2020.
Flying officer Arotule ta rasu ranar Talata 14 ga watan Yulin shekarar 2020 ta na da shekara 24, yayin da wata tsohuwar 'yar ajinsu da ta ganta ta juyo da baya cikin shauki da mararin ganinta don su gaisa ta kadeta da mota bisa kuskure, lamarin da ya sa ta yi ta zubar da jini har ta rasu.
Marigayiyar ta bada gagarumar gudunmowa wajen yaki da ‘yan bindiga dadi da ma ‘yan ta'adda a filin daga a arewa maso yammaci da arewa maso gabashin Najeriya, ta kuma samu yabo daga kwamandojinta akai-akai.
Ita dai dama can babban burinta shine ta zama soja. Marigayiya Arotule jajirtacciyar sojar sama mai hazaka ce da rundunar za ta jima ta na tunawa da ita, musamman duba da irin dimbin nasarorin da ta cimma a dan kankanen lokacin da ta yi a rundunar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5