Takaitaccen Tarihin Fitaccen Dan Siyasar Nijer Sanoussi Jackou

SANOUSSI JACKOU

An haifi Sanoussi jackou a 1940 a garin kornaka dake gundumar Dakoro. Ya yi firamari a Maradi kafin ya shiga sakandare a birnin Yamai. Daga nan ya wuce zuwa Jami’ar Cote d’ivoire da Jami’ar DiDjon a kasar Faransa, inda ya karanci fannin tattalin arziki.

Ya yi aiki a fadar shugaban kasa a zamanin Diori Hamani kafin ya koma Jami’ar Yamai don karantarwa. Daga nan Sanoussi Jackou ya wakilici Nijer a kungiyar CEAO wato UEMOA a birnin Ougadougou kafin ya dawo gida sai dai kuma watanni kadan bayan haka gwamnatin mulkin sojan kanar Seini Kountche ta kulle shi a gidan yarin Tilabery, inda ya shafe shekaru sama da 6 saboda zarginsa da yunkurin juyin mulki kafin daga bisani a wuce da shi zuwa gidan kason Dao Timi dake arewacin Bilma iyakar Nijer da Libya.

To amma guguwar dimokradiyar da ta girgiza kasashen Afrika a 1990 ta ba shi damar shiga harakokin shirya taron mahawarar kasa yayin da a dai gefe suka kafa jam’iyar CDS RAHAMA da wasu abokansa wace a karkashinta Mahaman Ousman ta lashe zaben shugaban kasa na 1992. A wancan lokaci Dan majalissar dokokin kasa Sanoussi jackou ya rike mukamin Mataimakin Kakakin Majalisa to amma barakar da aka samu ta sa ya kafa jam’iyar PNA Al’umma, wace ta hanyar ta ya kulla kawance da shugaba Bare Ibrahim Mainassara, inda ya rike mukamin ministan ilimi mai zurfi kafin su babe daga bisani.

A farkon shekarun 2000 Sanoussi Jackou ya yi adawa da gwamnatin Tanja Mamadou kasancewarsa daya daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyun hamayya a karkashin jagorancin Issouhou Mahamadou.

Dr Abdoulamalik Dan Galadima Haido Jackou rafani ne ga marigayin kuma ya yi bayani.

Alhaji Sanoussi ya shiga zaben da ya bashi damar zama dan majalissa a zamanin jamhuriya ta 6, wato a lokacin tazarcen Tanja domin a cewarsa siyasar kauracewa zabe abu ne da bai dace da cikakken dan siyasa ba.

Ministan koyar da ayyuka da sana’oin hannu, Kassoum Maman Moctar, ya yaba da halayyar mutunen da ya kira mai fafatuka don talakawa.

Mashawarci na musamnan a fadar shugaban kasa a tsawon mulkin Issouhou Mahamadou Sanoussi Jackou ya ci gaba da rike irin wannan matsayi a fadar shugaba Mohamed Bazoum har zuwa jiya Litinin, 18 ga watan yuli.

A ranar Alhamis 21 ga watan nan na Yuni ne za a yi jan’aizar sanoussi Jackou inda shugaban kasa Mohamed Bazoum da mukarraban gwamnatinsa zasu karrama shi kafin a yi masa rakiya don bizne gawarsa a garinsa na haifuwa wato Kornaka. Ya rasu ya bar mata 1 baturiya wato Francoise da ‘yaya 5 da jikoki a kalla 40.

Saurari cikakken rahoton Souleyman Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Tarihin SANOUSSI JACKOU.MP3