WASHINGTON D.C. —
Shugaban China, Xi Jinping, zai kai ziyara India domin yin wata ganawa wacce za’a yi ta ba’a hukumance ba a ranakun 11 da 12 ga watan nan na Oktoba.
Ganawar wacce za a yi a wani gari da ke kusa da birnin Chennai, za ta mayar da hankali ne wajen karfafa dangantakar kasashen biyu wacce ta yi rauni a ‘yan kwanakin nan.
Baraka ta farko da shugabannin biyu za su mayar da hankali akai, ita ce, tsoma baki da China ta yi kan matakin janye kwaryakwaryan ikon cin gashin kai da India daga yankin Kashmir, lamarin da Chinan ta soka, ita kuma India ta ji haushi saboda a cewarta, India ta yi katsalandan.
India da Pakistan dai na ikrarin mallakar yankin na Kashmir, lamarin da ya janyo har suka gwabza yaki sau biyu a baya.