Wasu daga cikin 'yanmatan nan 100 da shugaban Majalisar Dokokin Jihar zai aurar sun ce hankalinsu ya yi matukar tashi da suka samu labarin yunkurin hana auren nasu.
Muryar Amurka ta ziyarci wasu daga cikin Gidajen 'Yanmatan da ke garin Beri ta karamar Hukumar Mariga domin jin ta bakinsu akan wannan dambarwa da ta kunno kai.
Koda yake dai wasu rahotanni sun nuna cewa Ministan Matan Nigeriar Uju Kennady ta janye karar da shigar domin kalubantar wannan aure saboda dalilai na karancin shekaru da kuma auren dole.
Wasu daga cikin iyayen mata sun bayyanawa cewa suna cikin bakin cikin kokarin dakatar da wannan aure.
Garin na Beri dai na daya daga cikin garuruwan da suka sha fama da matsakar 'yan fashin dajin al'amarin da ya sa yanzu haka akwai tarin marayu da suka rasa iyaye maza.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai ba mu samu wani bayani ba daga gwamnatin jihar Neja ba akan lamarin amma Hon. Aliyu Bagga Muhammad, shugaban kansilolin karamar hukumar ta Mariga ya ba da tabbacin cewa babu maganar auren dole ga yaran.
Bayanai sun tabbatar cewa wannan daurin aure na 'yan mata 100 yana nan daram kamar yadda aka tsara a ranar 25 ga wannan watan na Mayu.