‘Yan Majalisar Wakilan Amurka sun kada kuri’ar amincewa da shigar da ‘karan babban atoni janar na Amurka William Barr da kuma tsohon lauyan fadar White House Don McGahn kan ‘kin amsa goron gayyatar da Majalisar ta yi musu dake da alaka da binciken kan shishshigin da kasar Rasha ta yi a zaben Amurka.
‘Yan Majalisun suna son a basu bayanai daga rahotan da mai bincike na musamman Robert Mueller ya yi, kan ko shguaban kasa Donald Trump ya yiwa shari’a karan tsaye ta hanyar yin katsalandan a binciken da aka yi, shi kuma McGahn sun son ya gurfana domin bada bahasi kana bin da ya faru cikin fadar White House.
Amincewa da shigar da ‘karan zai baiwa shugabannin ‘yan jam’iyyar Democrat a Majalisar Wakilai damar daukar mataki na gaba, idan sun zabi yin hakan daga baya.
Ranar Litinin, Majalisar Wakilai ta cimma yarjejeniya da ma’aikatar shari’a ta Amurka, da cewa zata mika musu muhimman bayanan da bincike Mueller ya tattara.