Yayin da tankiya tsakanin gwamnatin Kanon da majalisar kula da Zakka mai zaman kanta a jihar ke ci gaba da wakana kan batun mallakar harabar gidan Zakka na Kano, yanzu haka, al’umar yankin Darmanawa Layout na karamar hukumar Tarauni na zargin masarautar Kano da kokarin kwace filin Sallar Idi dake yankin wanda al’ummar musulmi suka kwashe kimanin shekaru 30 suna gudanar da ibada da kuma nufin sayar da shi ga ‘yan kasuwa domin gina gidaje.
Barrister Tijjani Yahaya shugaban kwamitin kula da wannan fillin masallacin idi na Darmanawa ya ce shi a fahimtar sa wadannan wuraren ba sa karkashin masarautar Kano, suna hannun gwamnatin jihar ne.
Koda yake shugaban kwamitin da aka ce majalisar masarautar Kanon ta kafa akan wannan takaddama Sarkin shanun Kano, Alhaji Shehu Mahmud ya ki cewa uffan dangane da batun, amma mataimakin Sakataren majalisar Alhaji Awaisu Abbas Sanusi ya ce mutane sun kai kuka su ga fadar sarki, kuma ya kafa wani kwamiti don yin bincike game da batun wanda a yanzu ana jira aga takardun shaida.
Sai dai ‘yan kwamitin filin idin na Darmanawa sunyi kukan rashin samun hadin kan da ya kamata daga kwamitin bayan mika korafin su ga masarautar ta Kano.
Barrister Tijjani Yahaya yace, muddin suka gaza cimma masalaha da masarautar ta Kano, to basu da zabi illa gurfana a gaban kuliya.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Your browser doesn’t support HTML5