Shugaban Hukumar kula da harkokin albashi da hakkokin ma'aikata ta kasa, Richard Egbule, ya bayyana wa manema labarai a rubuce cewa, kudaden da kungiyoyin kwadago suke nema a hannun gwamnati ya yi yawa.
Richard ya ce, gwamnati ta yarda ta yi karin albashi ga kananan ma'aikata daga mataki na daya zuwa na bakwai, amma daga mataki na takwas zuwa sama, Naira dubu goma ne za a iya karawa. Sakataren tsare tsare na kungiyar kwadago ta ULC Kwamrad Nasiru Kabir, ya ce, ba haka yarjejeniyar ta ce ba, ya kara da cewa, an amince da karin albashi ne gaba daya, ba wai wani bangare ya samu kuma wani bangare ya rasa ba ne, kuma karin na dukan ma'aikata ne har da shugaban 'kasa kanshi.
To sai dai Kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Yusha'u Aliyu ya ce, doka ce ta ce a yi wa ma'aikata karin albashi daga lokaci zuwa lokaci, kuma gwamnati ce ta ke da hurumin yin hakan, bayan ta yi karin sai kuma ta daidai ta farashin kayayyaki a kasuwa domin a samu nasarar karin.
Amma Babban Daraktan da ke kula da Ma'aikatar Al'adun Gargajiya ta Kasa, Olusegun Runsewe yana ganin ba karin albashi ne kan gaba a yanzu ba, shi yana ganin ya kamata a daidai ta harkokin zaman lafiya da zamantakewa tukuna, kafin a yi maganan karin albashi.
Madam Christiana Gokir, ta Ma'aikatar Watsa Labarai ta kasa ta ce, tun ba a yi karin ba, kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi a kasuwanni, inda ta yi kira ga Gwamnati da ta yi takatsantsan wajen yin karin albashin, saboda karamin ma'aikaci ya ci moriyar sa.
Ga rahoton wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda daga Abuja Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5