Shugabannin jam’iyyun Republican da na Democrat a majalisar dokokin Amurka, na kokarin ganin an samu matsaya. Yayin da alamu ke nuna cewa shugaba Donald Trump, na yunkurin janyewa daga barazanar da ya yi ta rufe ma’aikatun gwamnati a wannan makon.
A makon da ya gabata ne shugaba Trump ya shaidawa ‘yan jarida cewar, “Abun alfahari ne gare shi ya kulle ma’aikatun kasar” idan har ba su amince da bukatarsa ta neman a gina katanga ba. Yana mai cewa, “za mu ga mai zai faru, kada a yi riga malam masallaci. Muna da bukatar tsaro akan iyakokinmu.”
A ranar Juma’a mai zuwa, ma’aikatun gwamnatin tarayya za su fara dakatar da wasu ayyuka marasa muhimmanci, idan har ‘yan majalisun da fadar White House ba su cinmma matsaya ba, akan kudaden da gwamnati za ta kashe cikin dogo ko gajeran zangon lokaci.
Ma’aikatan gwamnati sama da 800,000 abun zai shafa, wasu daga ciki za su yi aiki ba tare da an biya su ba.
Wannan abu ne da babu wanda zai so ganin ya faru a dai-dai lokacin da ake shirin bikin Kirsimeti.
Shugaba Trump na bukatar dallar Amurka billiyan $5 don gina katanga tsakanin kasar da kasar Mexico. Amma, ‘yan majalisar wakilai da ta dattawa sun ki amincewa da rokon.