Ministar Kudi da tsaretsare Zainab Shamsuna Ahmed ta ce akwai sharuda na yin amfani da wanna shawarar da IMF din ta bayar. Ta bayyana cewam karkashin shirin, za a ba mutane marasa galihu miliyan 40 a kasar, Naira dubu 5-5 a kowane wata, domin rage masu radadin biyan kudin sufuri.
To sai dai Majalisar Dattawa , da masanan tattalin arziki, da kwararru a fanin zamantakewan dan Adam sun ce abin ba zai ma yiwu ba.
Kwamitin kula da Kassafin Kudi a Majalisar Dattawa karkashin jagoranci Sanata Adeola Olamilekan Solomon ya ce Kuduri kasafin kudi na shekara 2022 ya kunshi tallafin man fetur, amma babu wani tanadi na tallafin sufurin da ake shirin yi na Naira 5,000 ga wasu yan Najeriya miliyan 40, wanda zai kai Naira triliyan 2.4 a duk shekara. .
Olamilekan ya ce in har za a bada irin wannan tallafi to sai an aika da takarda zuwa Majalisar kasa don ganin yadda zai yiwu a ba 'yan Najeriya su Miliyan 40 alawus din sufuri.
Amma ga kwararre a fani tattalin arziki Abubakar Ali yana ganin akwai abin dubawa a wannan yunkurin bada tallafin kudin sufuri, domin a baya ma an ce an bada tallafin ciyar da dalibai a gida na makudan kudade a lokacin annobar korona Bairus, in ba a yi hankali ba, wannan zai bi hanyar da wacan tallafin ya bi.
Shi kuwa Tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa Komred Isa Tijjani ya ce a yi la'akari da cewa Ma'aikatar man fetur ta kasa ce kadai ke da hurumin shigo da man fetur cikin kasa domin gudun kar 'ya kasuwa su tsawala kudi idan an yarda su shigo da man. Tijjani ya ce tambaya ce yake da ita ga NNPC, wai a ina ta ke samun kudin shigowa da tattacen man fetur?
Amma Ministar Kudi da Tsare Tsare Zainab Shamsuna Ahmed ta mayar da martani cewa cire tallafin man fetur ya zama dole, kuma da Gwamnati da abokan aikin ta sun amince da shawarar cire tallafin a wani mataki da zai ba kasa daman farfadowa da wuri, kuma haka zai ba yan kasa dama na samun saukin rayuwa.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5