Takaddama Ta Kaure Tsakanin Yan PDP Da APC A Majalisar Dattawa

PDP-APC

Gamaiyar yan adawa ta PDP a karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye Enyinanya Abaribe sun baiyana damuwarsu akan yadda Jamiyar APC mai mulki a karkashin shugaba Mohammadu Buhari ta kasa kawo karshen rashin tsaro a kasa, wanda shi ne muhimmin dalilin Kampe din su a shekara 2015.

Sanata Abaribe ya ce APC ta bari rashin tsaro ya yadu a kowane sashi na kasa, don haka a matsayin su na wakilan jama'a suna kira da a gaggauta kawo karshen wannan matsala ta tsaro baki dayan ta.

Enyinanya Abaribe ya kara da cewa baya ga batun tsaro, wani abu da ya dauki hankalin su shi ne batun farfado da tattalin arzikin kasa, suna ganin gwamnati na neman buga kudi a matsayin hanyar habbaka tattalin arzikin kasa wanda yin haka ba daidai ba ne, zai kara tashin farashin kaya ne da kuma kara karya darajar kudi.

To sai dai Gamaiyyar yan Jamiyar APC mai mulki a karkashin jagorancin Shugaban Masu rinjaye Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar sun yi watsi da abin da suka bayyana da cewa, bayanan yan adawan na rashin gaskiya da adalci.

Karin bayani akan: Sanata Yahaya Abdullahi, APC, PDP, DSS, Jihar Zamfara, Nigeria, da Najeriya.

Bisa ga cewar su, a lokacin Mulkin PDP ne Boko Haram suka shigo Najeriya, kuma dukan matsalar tsaro da ta auku a Jihar Zamfara har ta mamaye sauran jihohin Arewa maso yama ya fara ne a karkashin su.

Sanata Yahaya Abdullahi ya ce duka gwamnatoci da suka shude basu dauki kwararan matakai ba ne ya sa wannan mulkin Jamiyar APC ta gaji matsalar, kuma tana ta kokarin magancewa.

'Yan jam'iyar APC sun bayyana cewa, ainda ba za su lamunta ba shi ne mayar da batun tsaron ya zama ta siyasa. Sanata Yahaya ya ce matsalar ta shafi kowa da kowa, babu banbancin siyasa ko jinsi ko yanki. Ya ce shekarun sa na haihuwa 70 yanzu , shi bai taba ganin gwamnati da ta ba kowa damar walwala kamar wannan gwamnati ta APC ba.

Akan batun farfado da tattalin arziki, Sanata Yahaya Abdullahi ya ce kasa ta tsinci kanta a wani hali na bullar cutar coronavirus shi ya sa aka samu durkushewar tattalin arziki kaman yadda ya shafi ko wacce kasa a duniya. Inda yayi kira da cewa yanzu ana sayar da gangan danyan man fetur akan dala 70 maimakon dala 45 da aka gina kasafin kudin bana akai.

Saboda haka suna kira ga Shugaban Kasa da ya kawo kwaryakwaryar kasafin kudi domin a yi amfani da rarar da aka samu wajen farfado da tatalin arzikin kasar.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddama Ce Ta Faru A Tsakanin Yan Adawa Da Yan APC A Majalisar Dattawa