Takaddama Game Da Taron Majalisar Matasan Nijar

NIGER

‘Yan adawa a babban birnin Yamai sunyi suka da kakkausar murya ga majalisar matasa ta jamhuriyar Nijar, kan cewa ‘ya ‘yan masu kudi da mulki ne kadai ke cikin majalisar.

Yayin da Majalisar Matasan ke fara wani babban taronta, ‘yan adawa na ganin majalisar bata da wani amfani ganin irin halin da mutane ke ciki, kuma kasar na fama da matsin tattalin arziki.

A cewar Alhaji Dange Mai Hula na jam’iyyar MODEM LUMANA, cikin ‘yan majalisar babu wanda ya san ciwon talaka, kuma duk abubuwan da ake kullawa babu wani abin da zai shafi ci gaban talaka, face barnar dukiyar ‘kasa.

Da yake mayar da martani kan wannan batu Alhaji Tsalaha ‘Dan Ba’u na jam’iyyar PNDS Taraiya, ya musunta wannan zargi da ‘yan adawar suka yi wa majalisar matasan ta ‘kaasa, in yake cewa babu kanshin gaskiya a ciki. Ya kuma ‘kara da cewa duk wanda ya dubi wannan Majalisa zai ga akwai ‘ya ‘yan talakawa da ‘ya ‘yan masu kudi a cikinta.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Mamman Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddama Game Da Taron Majalisar Matasan Nijar - 2'57"