ShinTa Yiwu Zabe Ba Tashin Hankali

Tashin hankali bayan zabe

Hukumar zabe ta INEC da wasu kugiyoyi sun gudanar da taron 'yan takara daga duk jam'iyyun akan yin yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya lokacin zaben da bayansa.

Taron da aka yi a Abuja ya samu jagorancin Chief Emeka Anyaoku tsohon babban sakataren kungiyar kasashe renon Ingila.

Mr Koffi Anan tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya shi ma ya kasance a taron. Ire-irensu sun halarci taron ne domin sa ido akan yarjejeniyar da 'yan takaran da jam'iyyunsu zasu sama hannu.

Dr Mani Ibrahim daya daga cikin 'yan takaran neman mukamin shugaban kasa na jam'iyyar Africa Development Congress ko ADC a takaice, yace yarjejeniyar tana da kyau amma kuma akwai abubuwa da dama da yakamata a yi kafin tayi aiki ta kuma yi tasiri.

Yace babu anfani a yi yarjejeniya kana a cigaba da yin abubuwa kaman na da. It yarjejeniyar bata fadi abun da za'a yiwa wanda ya karyata ba. Damuwa da halayen 'yan takaran daga lokacin yarjejeniyar zai fi mahimmanci.

Zabe mai adalci mai inganci ya makata a mayarda hankali a kai. Zai fi yarjejeniya yin tasiri. Dr Ibrahim yace domin idan mutane suka lura cewa zaben ba'a yishi da adalci ba zai yi wuya a hana barkewar tashin hankali. Dole hukumar zabe ta tabbatar an yi adalci kuma ba'a ba kowane dantakara galaba a inda bai kamata ya samu ba.

A waje daya kuma Dr Jibril Ibrahim tsohon shugaban cibiyar dimokradiya ta Najeriya ya bayyana cewa lallai yarjejeniyar tana da kyau amma tilas ne a yi zabe mai adalci tunda shi ne hanya mafita da zai iya kawo karshen kowane irin tashin hankali da za'a iya samu a kasar.Yayi misali da zaben da aka yi a jihar Ondo lokacin shugabancin Shagari. Rahoton binciken zaben ya nuna cewa ita hukumar zabe ta lokacin bata yi gaskiya ba. Tayi coge tare da taimakon 'yansanda da jami'an tsaro. Abubuwan da suka jawo mummunan tashin hankali ke nan a jihar.

Idan aka yi zabe mai inganci, kowa ya ga gaskiya aka bi ba za'a samu tashin hankali ba. Amma muddin mutane suka gane ba'a yi adalci da gaskiya ba, ba zasu yadda ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ta Yiwu? Zabe Ba Tashin Hankali- 5' 20"