Mayakan dake yiwa Bashar al-Assad yaki tare da goyon bayan Sojojin Rasha sun fito ne daga kasashe daban daban
WASHINGTON DC —
Gwamnatin Syria ta nemi Iran ta sa kai ta dauki lalurar kula da kuma biyan albashin dubban mayakan Shi’a da ke yaki tareda sojan Rasha a famar da suke na goyon bayan shugaban kasar ta Sham, Bashar al-Assad.
Wata kafar watsa labaran duniyar gizo ta gwamnatin Syria din mai suna Zaman Al Wasel, ne ta ruwaito cewa ta sami wani rubutaccen bayani daga ma’aikatar tsaro inda a ciki ake nuna cewa Syria ta gama yanke shawarar hannunta wa Iran hakkin biyan wadannan dubban mayakan na Shi’a da suka fito daga kasashen ketare daban-daban.
A inda aka fiton nan, galibi akan samu biyan albashin wadanan mayakan ne daga aljihun gwamnatocin Iran din da Syria da kuma na kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon.