Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Sake Takawa Dokar Hana Shigar Baki Amurka Birki


Masu zanga-zanga a kofar kotun koli a jihar Virginia.
Masu zanga-zanga a kofar kotun koli a jihar Virginia.

Babban lauyan gwamnatin Amurka Jeff Sessions yace zai sa kotun kolin kasar tayi nazarin hukumcin da kotun koli ta yanke da ya takawa umarnin shugaba Donald Trump birki, na takaitawa wadansu kasashe shida da galibi Musulmi ne shiga Amurka.

Session ya fitar da sanarwa jiya alhamis cewa, umarnin shugaba Trump yana karkashin ikon tsaron kasa.


Ya kara da cewa, ma’aikatar shari’a bata goyi bayan hukumcin kotun da ra’ayi ya banbanta ba, data takawa yunkurin shugaban kasa na kara ingancin tsaron kasar birki. Yace ba a son aga shugaban kasa ya kyale mutanen da suka fito daga kasashen dake daukar nauyin ta’addanci su shiga Amurka, sai ya hakikanta cewa, an iya bincikesu an kuma gamsu cewa basu da hatsari ga Amurka.

A hukuncin da aka yanke jiya alhamis, kotun daukaka karar tace a bayyana yake cewa, umarnin ba komi bane, face alkawarin da shugaba Trump ya yi kafin, da kuma bayan zabe, na nunawa Musulmi wariya.
Galibin alkalan kutun su goma sha uku, sun yi misali da rubuce rubucen Trump a shafinsa na twitter da hirarraki a tashoshin talabijin,da kuma bayanan da aka buga a shafinsa na yakin neman zabe a matsayin shaidun manufarsa.
Alkalan kotun guda uku basu goyi bayan hukumcin kotun ba bisa hujjar cewa, babu inda aka ambaci addini a zartarwar ta shugaban kasa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG