Syria: Hare-haren Jiragen Saman Rasha Sun Hallaka Mutane 18

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Masu fafutuka a Syria sun ce, wasu hare-haren sama da ake kyautata zaton jiragen Rasha ne suka kai, sun kashe akalla mutane 18 kana suka jikkata wasu 40 a arewacin kasar.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a wata kasuwa mai cike da mutane.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights da ke Burtaniya, wadda kuma ke sa ido akan rikicin na Syria, ta ce hare-haren an kaisu ne a wani gari da ake kira Ariha da ke kusa da Lardin Idlib mai tazarar kilomita 20 da iyakar Turkiyya.

Wannan yanki dai na hanun mayakan kungiyar Nusra ne da ke da alaka da kungiyar Alqaeda, kuma ba yanki ba ne da ake samun mayakan IS.

A watan Satumba, Rasha ta fara kai hare-hare a Syria, lamarin da ke samun sukar Amurka da sauran kawayenta da ke kai hare-hare akan mayakan IS.

A wata tattaunawa da aka yi a jiya Lahadi a birnin Damascus, wani babban jami’in kasar Iran Ali Akbar Velayati da shugaban Syria Bashar al Assad, sun ce abokanan gabarsu sun kara samun tallafin kudade da makamai yayin da dakarun gwamnati ke samun goyon bayan Iran da Rasha, kamar yadda kafar yada labana kasar ta tabbatar.