Syria: Amurka Ta Dora Alhakin Harin Makami Mai Guba Akan Rasha

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, ranar 9 ga watan Agusta 2017.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, ranar 9 ga watan Agusta 2017.

Amurka ta dora alhakin harin makami mai guba da ake zargin dakarun Syria da kai wa a wasu yankunan fararen hula da ke Syria, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama.

Amurka ta yi kira ga Rasha da ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa gwamnatin Syria cikin gaggawa, ta kuma yi aiki tare da sauran kasashen Duniya domin a kaucewa munanan hare-haren da ake kai wa da makamai masu guba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert ce ta bayyana hakan, a wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, tana mai cewa Amurka na bibiyan wani rahoto da ya fito a ranar 7 ga Afrilu.

Rahoton ya nuna cewa an yi amfani da makami mai guba akan wani asibiti da ke garin Douma na Syria.

Sanarwar ta kara da cewa, “Rasha” ce ke da alhakin wannan hari, saboda goyon bayan da take bai wa gwamnatin ta Syria, inda ake kaikaitar dumbin fararen hula, ta hanyar sike numfashin al’umar yankin da makami mai guba.

‘Yan tawaye suna zargin cewa dakarun gwamnatin sun jefa wani kuttun bama-bamai mai dauke da sinadarai masu guba a ranar Asabar, lamarin da ya halaka mutane da dama.