Super Eagles Zata Doke Pharoahs A kaduna Inji - Amaju Pinnick

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF tace zata yi duk abinda zata iyayi domin ganin cewa kungiyar ‘yan wasan Super Eagles ta sami nasarar doke kungiyar ‘yan wasa ta Egypt a karawar da kungiyoyin biyu zasu yi a kaduna.

Najeriya zata marabci kungiyar ‘yan wasan Pharoahs, wadda ta dauki ragamar jagoranci a rukunin G na shiga wasannin zakarun cin kofin Afirka AFCON na shekarar 2017, da maki shidda a wasanni biyu a filin wasa na Ahmadu Bello Stadium dake Kaduna.

Kungiyar Super Eagles ta yi kasa a gwiwa a wasan zagaye na uku kamar yadda shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriyar Mr Amaju Pinnick ya ce basa son hakan ya sake afkuwa.

Shugaban ya fadawa mujallar completesportnigeria cewar suna mayar da hankali akan karawar da zasu yi da kasar Misira ne, kuma sunsan alfanun hakan, domin suna so su sami shiga wasannin cin kofin zakarun Afirka mai zuwa da za’a buga a kasar Gabon.

Ya kara da cewa yasan har yanzu ‘yan Najeriya basa jin dadi akan kashin da kungiyar ‘yan wasan ta sha , kuma baza su sake yadda hakan ta kara faruwa da suba.

Kasar Misira ce zata fuskanci najeriya a rukunin wasan, dan haka Pinnick ya ce dan haka dole ne su yi duk yadda zasu yi domin ganin sun sami nasara akan su.