Super Eagles Na Bukatar Kwararren Mai Tsaron Raga

Tsohon mai bada shawara ga hukumar kwollon kafa ta Najeriya wato (NFA), Tunde Disu, ya ce kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles tana bukatar mai tsaron raga da ya dace da zamani.

Disu ya bayyana haka ne yayin da ya tattauna da kamfanin dillanci labarai na Najeriya wato (NAN), a yau Talata lokacin da yake magana akan irin kura kuran da mai tsaron raga na Super Eagles, Daniel AKpeyi ya yi.

Disu shine tsohon mataimakin mai horaswa Otto Gloria, mai horarwar da ya lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika a shekarar 1980, ya ce kungiyar Super Eagles tana bukatar mai tsaron raga da ya ke da kwarewa sosai.

Sai dai kuma yayi tamabaya cewa “muna matukar bukatar wani mai tsaron raga a yanzu, kuma idan zan yi tambaya, mene ne aikin masu horar da mai tsaron raga da kuma masu taimaka masa da muke da su a sansanin da suke daukan horo?

Sannan kuma yace ya kamata masu horaswa yanzu su zagaya don samo masu tsaron gida, kuma bai kamata mu zama masu saka ci ba, ya kara da cewa bai kamata ya zama mun zauna da abunda muke da shi ba, ya kamata mu duba cikin 'yan wasan mu na gida.