A shirye shiryen ta na fafatawa a gasar cin kofin duniya na 2018, da za a yi a kasar Rasha cikin watan yuni 2018, Najeriya karkashin jagoranci kocinta Gernot Rohr, ya fidda jerin sunayen ‘yan wasa 30 domin tun karar gasar cikin su harda dan wasan gaba na Kano Pillars Junior Lokosa, dan wasan da yafi kowa zurara kwallaye a gasar Firimiyar Najeriya, na bana a yanzu haka ya jefa kwallaye 18 a cikin wasa 20 da ya buga.
Cikeken jerin sunayen ‘yan wasan na Super Eagles sune kamar haka
A bangaren masu tsaron gida akwai, Francis Uzoho (Deportivo La Carina), Dele Ajiboye (Plateau United), Daniel Akpeyi (Chippa United), Ikechukwu Ezenwa (Enyimba FC).
Masu tsaron baya kuwa akwai
William Troost Ekong (Bursaspor), Leon Balogun (Mainz), Chidozie Awaziem (Nantes), Kenneth Omeruo (Kasimpasa), Shehu Abdullahi (Bursaspor), Tyrone Ebuehi (Ado den Haag), Ola Aina (Hull City), Elderson Echiejille (Cercle Brugge), Brian Idowu (Amkar Perm), Stephen Eze (Lokomotiv Plovdiv).
Sai kuma ‘yan wasan tsakiya
John Mikel Obi (Tianjin Teda), Joel Obi (Torino) Ogenyi Onazi (Trabzonspor), Etebo Oghenekaro (Las Palmas) , John Ogu (Hapoel Beer Sheva), Wilfred Ndidi (Leicester City), Uche Agbo (Standard Liege), Mikel Agu (Bursaspor ).
A bangaren masu zurara kwallaye kuwa sun hada da
Alex Iwobi (Arsenal), Victor Moses (Chelsea), Odion Ighalo (Changchun Yatai), Kelechi Iheanacho (Leicester City), Ahmed Musa (CSKA Moscow), Junior Lokosa (Kano Pillars), Moses Simon (KAA Gent), Simy Nwankwou (Crotone).
Sai dai cikin jerin sunayen babu wasu ‘yan wasa da ake tsammanin su irin su Brown Ideye, Dele Alampasu, Anthony Nwakaeme, Henry Onyekuru, Victor Osimhen da kuma Kayode Olanrewaju.
Your browser doesn’t support HTML5