Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohamed Salah dan kasar Masar ya kasance gwarzon dan wasan kwallon kafa ta bana agasar Firimiya lig na kasar Ingila na shekara 2017/2018.
Salah ya samu wannan nasaranne bayan da ya taimaka wa kulob dinsa Liverpool ta kammala a matsayi na 4 a kakan wasa ta bana. Inda ta samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai na shekara mai zuwa, kuma zata buga wasan karshe a bana na zakarun turai da kungiyar Real Madrid na Spain ranar 26 gawatan Mayu 2018.
Haka kuma dan wasan ya kafa tarihi a bangaren zurara kwallaye a bana inda ya jefa kwallaye 44 a cikin wasanni 51 da ya buga wa kungiyarsa ta Liverpool a dukkanin wasanta na bana.
A bangaren Firimiya lig ya zurara kwallaye 32 a wasanni 38 Inda ya karya tarihin Tsofaffin yan wasa irin su Alan Shearer wadda yaci kwallaye 31 wa kungiyar Blackburn a shekara 1995-96, Cristiano Ronaldo mai kwallaye 31 a Manchester United a shekara 2007-08, Luis Suarez kwallaye 31 a Liverpool shima shekara 2013-14.
Alan Shearer, ya sake zurara kwallaye 31 a Blackburn shekara 1994-95, Andy Cole, kwallaye 31 a kungiyar Newcastle United a 1993-94.
Facebook Forum