Sun Amince su Karbi na Goro Gabanin Gasar cin Kofin Kwallo Kafa na Duniya

Chuck Blazer

Shahararen dan wasan kwallon kafa kuma tsohon kaftin din Ingila David Beckam, ya shiga ayarin masu yin Allah wadai da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, dagane da batun cin hanci da rashawa da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka wato FBI, ta zakudo.

Beckam, yace wasu abubuwan da suka faru a hukumar abun takaici ne kuma marasa karbuwa, a wasan da duk muke kauna.

Wasan kwallo kafa bana wasu mutane ‘yan kalilan bane, na miliyoyin jama’a ne masoya wasan da suka basu a fadi duniya, in ji Beckam.

Yana mai cewa lokacin canji yayi a hukumar ta FIFA, kuma yakamata jama’a suyi ma’am da canjin.

Wani tsohon dan kwamitin zartarwa na hukumar ta FIFA, Chuck Blazer, ya bada shedar cewa shi da wasu sun amince su karbi na goro,gabanin cin kofin kwallo na duniya da aka buga a Faransa a shekarar 1998, da kuma wanda aka buga a Afirka ta kudu.