Rahotannin da ke cewa, Sule Lamdo da wasu manyan Jam'iyyar PDP na arewaci da kudancin Najeriya na gudanar da tarukan sirri domin kirkiro da sabuwar Jam'iyya ko kuma su sauyawa PDP suna.
A hirar Sule Lamido da wakilin Muryar Amurka na Kano Mahmud Ibrahim Kwari, Alhaji Sule Lamido ya kuma tabo sauran batutuwan da suka shafi Jam'iyyar PDP da kuma makomar siyasar Najeriya.
Da farko an tambayi Lamido cewar tunda shi aka ce yana jagorantar wannan tattaunawa to ya abin yake?
Lamido dai yace shi kanshi bai san abinda yake faruwa ba saboda kamar yadda kowa yake jin labarin wannan taro shima haka yake jin labarin a kafofin yanar gizo. Inda har ma ya nemi da abar yin irin wannan abu na yaudara.
Wakilin Muryar Amurka ya yiwa Lamido tambayar cewa, ‘yan PDP sun firgita musammam ta la’akari da rashin samun madafun iko ko asarar madafun iko, to me kukeyi a yanzu domin a saita ita jam’iyyar?
Ya amsa da cewa, “yan Najeriya na la’akari da ‘yan PDP ko ‘yan APC akan matsayin mukami” ya ci gaba da cewa duk masu jefa kuri’a na birni ko na kauye abinda suke so shine ayi musu aiki, ba wai mukami ba, masu maganar mukamai mukamai ‘yan kadan ne.
Saurari cikakkiyar hirar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido.
Your browser doesn’t support HTML5