Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Gasa Buredi A Jihar Borno Zasu Fara Yajin Aikin Kwanaki Uku


Gasasshen Burodi
Gasasshen Burodi

Kungiyar masu gasa Buredi da ke jihar Borno, zasu dakatar da gasa Buredi har na tsawon kwanaki uku, a wani mataki na nunawa gwamnati irin matsalolin da suka shiga, musammam ma na tsadar kayayyakin gasa Buredin.

Wannan kungiya ta masu gasa Buredi dai sunce sun ‘dauki wannan matakin ne don nunawa jama’a cewa suna shirin ‘kara kudin Buredi gaba ‘daya.

Sakataren kungiyar masu gasa Buredin Mallam Bukar Mustapha, ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna fuskantar matsaloli da dama, musammam ma tashin gwauron zabin da kayayyakin gasa Buredi yayi. Kuma tamkar suna gasa Buredin ne kawai, amma ba don riba ba, don haka ne suka gudanar da wani taro da daukar matakin dakatar da gasa Buredin har na kwanaki uku.

Mallam Bukar ya baiwa mutanen jihar Borno hakurin dakatar da gasa Buredin har na kwanaki uku, domin suna son biredin da yake cikin kasuwa ya kare, domin zasu fito da wani sabon tsari da kara kudin Buredin.

Wasu al’ummar jihar Borno sunyi bayani kan yadda suke ganin za a shiga matsala ga masu sara da masu sayarwa a birane da kauyuka.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya aiko mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG