Sule Lamido Na Hannun ‘Yan Sandan Najeriya

Alhaji Sule Lamido.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, a gidansa dake Kano.

Gwamnatin jihar Jigawa ce ta kai karar tsohon gwamnan gaban rundunar ‘yan Sanda ta Najeriya, bisa zargin tunzura jama’ar Jigawa su bijirewa zaben kananan hukumomi da hukumar zabe ta jihar zata gudanar ranar daya ga watan Yulin bana.

A jiya Lahadi ne dai da missalin karfe ‘daya na rana Sule Lamido ya amsa gayyatar jami’an shiyya ta ‘daya ta rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Kano.

Cikin takardar korafin gwamnatin ta Jigawa na zargin Sule Lamido da yunkurin tunzura ‘yan jigawa a yayin zaben ‘kananan hukumomin jihar da zai wakana a watan Yuli mai zuwa.

Kakakin shiyya ta ‘daya ta rundunar ‘yan sandan da ke Kano, DSP Sambo Sokoto, ya tabbatar da cewa gwamnatin jigawa ta shigar da korafin cewa tsohon gwamnan yana tara jam’a yana maganganun da za su iya tayar da hankulan jama’a.

Tun a jiya jami’an ‘yan sandan suka gudanar da binciken kwakwaf a gidan Sule Lamido dake garinsu a Bamaina da kuma gidansa na Kano. Amma dai rahotanni na nuni da cewa babu wani abu da aka bankado.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Sule Lamido Na Hannun ‘Yan Sandan Najeriya - 3'31"