Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki Ta Zargi Kamfanin YEDC


Injinan Kamfanin Sarrafa Wutar Lantarki
Injinan Kamfanin Sarrafa Wutar Lantarki

Kungiya ma’aikata masu sarrafa wutar lantarki ta ‘kasa reshen arewa maso gabas ta ce mambobinta shida sun rasa rayukan su, saboda rashin kariya a lokacin da suke bakin aiki sakamakon sakaci da neman riba fiye da kima.

Sakataren kungiyar kwamrad Patrick Vigo, ya furta haka ga taron ‘yan jaridu a Yola fadar jihar Adamawa da yake gabatar korafe-korafen kungiyar, inda kungiyar take zargin kamfanin samar da wutar lantarki na YEDC mai kula da shiyyar arewa maso gabas da sanya ma’aikata yin aikin da ba su da kwarewa akai, don kaucewa biyan albashi da ya kamata ya biya kwararru wanda ke jawowa mambobinta hallaka.

Baya ga rashin martaba rayuka, kungiyar tana zargin kamfanin da sauwala kwangilar sayan motoci hudu kirar Hilux uku da Toyota daya da farashinsu ya kai sama da naira miliyan saba’in da daya wanda ta ce ya kusa ninka farashinsu a kasuwa. Da kuma kuntatawa ta hanyar sallamar daya daga ma’aikatanta sakamakom wata almundahana ta sayan motar alfarma da ya bankado.

Ma’aikacin da kamfanin ya sallama Mahmood Dan Malam Ibrahin, a hirar sa da muryar Amurka ya ce kafin korarsa, kanfanin ya bukace shi ya janye takardar da ya rubuta kan badakalar ko a bakin aikinsa, wanda ya ce “ba zan yi ame na lashe ba” a martanin da ya baiwa kanfanin bayan an yi masa sauyin wurin aiki zuwa Maiduguri lokacin da yaki da boko Haram ke zafafa.

Zarge-zargen da babban manajan kamfanin sarrafa wutar lantarki shiyyar arewa maso gaba Injiniya Umara Baba Mustapha, ya ce babu kanshi gaskiya a ciki, a cewarsa motocin da ake batunsu ma’aikata samar da wutan lantarki ta tarayya ce ta saye su biyo bayan bukatarsu da kanfanin ya nuna.

Manajan kanfanin ya ce babu wanda ya yi asarar ransa lokacin da ya ke bakin aikin, yana zargin ‘ya’yan kungiyar da kwadayi abin da inji shi ke jefa su cikin hatsari.

Cikin takardar da ke dauke da korafe-korafen, kungiyar ta yi barazanar a shirye take ta ankarar da hukumomin da ke yaki da zarmiya, cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC kan irin badakalar da ake toyawa a kanfanin idan ya ki daukar mataki akan su.

Saurari rahotan Sunusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG