Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Ya Jaddada Muhimmancin Rufe Iyakokin Kasa

Babban Sufeton 'Yan Sanda Muhammad Adamu

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya karfafa muhimmancin rufe kan iyakar Najeriya da kasashe makwabtanta, domin cimma muradun aiyukan tsaro.

Sufeto Adamu wanda ke magana bayan taro kan tsaro a fadar Aso Rock, ya fito fili ya bayana dalilan rufe kan iyakar, inda ya ce abin ya wuce batun fasa kwabrin kayan abinci da lamuran kasuwanci, ana hakan ne domin samun dakile shigo da makamai.

Kakakin shugaba Buhari Garba Shehu ya taba yin bayani kan yadda kasashen tafkin Chadi ke hada kai da Najeriya don murkushe ta’addanci da tuni ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da dukiya.

Ministan Cikin Gidan Nijar Muhamed Bazoum

Shima ministan cikin gidan Nijar Mohammed Bazoum yayi magana a taron ECOWAS/Cedeao a Abuja da aka kammala, na bukatar bude iyakar.

Saurari karin bayani cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Ya Jaddada Muhimmancin Rufe Iyaku