Sudan Ta Kudu Taki Amincewa Da Wasu Kudurorin Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu tace ba zata lamunta da yarjejeniyar da ake rarrabawa ba a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda ke kiran cewa a aika da wasu sojojin yankin raya gabashin kasashen Africa zuwa birnin Juba dama wasu sassan kasar da yaki ya daidaita ba.

Ministan yada labarai na kasar Michael Makuei, yace kasar ba zata yarda da wannan sojojin ba musamman suna karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ne dake aiki a kasar, domin wannan zai rage wa kasar martabar ta ta kasa mai cikakkiyar yancin kanta.

majalisar dinkin duniya dai ce ta samar da wani kudiiri wanda aka tattauna a zauren taron kwamitin tsaro na majalisar dikin duniya a New York.

Suma shugabannin kasashen yankin gabashin Africa sun gudanar da taro a Adis Ababa domin tattauna yadda za a bada wannan kariya daga yankin kasar ta Sudan ta Kudu take.

A cikin satin data gabata ne dai a New York kwamitin tsaro ta majalisar dinkin duniya ta kara tsawon wa’adin da ya baiwa kwamitin na musammam mai aiki a kasar ta Sudan ta Kudu, wanda kuma idan bata bi wannan tsarin ba wa’adin zai kai karshe gobe juma’a.

Sai dai kafin gobe din shugabannin yankin kasashen Africa ta gabas da abokan su suna sake duba wannan damar tare da yi mata kwaskwarimar data dace.

Wasu daga cikin batutuwan da ake tattaunwa a wannan taron sun hada da ko dai a bar kwamitin nan mai aiki na musammam a kasar ta Sudan ta Kudu damar hana saye ko sayar da makamai da jiragen sama ga Gwamnati ko kuma kungiyar’yan tawaye, musammam wadanda ke fada karkashin SPLA, Sudan People Liberation Army. Ko kuma A’a