WASHINGTON D.C. —
Bayan ganawa ta tsawon sa’o’i uku jiya Laraba a gidan gwamnati na Sudan Ta Kudu, Shugaba Salva Kiir da jagoran ‘yan adawa Riek Machar, sun yi alkawarin warware dukkan sauran matsalolin da su ka rage da ke shafar shirin kafa gwamnatin hadin kan kasa a watan Nuwamba.
Shugabannin biyu na cike da murmushi yayin da su ke shan hannu da kuma daukar hotuna tare a harabar Gidan Gwamnati, to amma babu wani daga cikinsu da ya bayyana cimma wasu sabbin yarjajjeniyoyi.
Daga cikin batutuwan da ba a daddale ba a yarjajjeniyar da aka cimma bara, har da batun yawan jahohi da kuma iyakokinsu da kuma tsarin tsaron kasa da kuma rawar da dakarun ‘yan tawaye da na gwamnati za su taka a ciki.