Sudan Ta Kama Nakiyoyi Masu Karfin Ruguza Birnin Khartoum

Shugaban Sudan Janar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan

A wani al'ami mai nuna alamar har yanzu da sauran rina a kaba game da rigimar shugabanci, siyasa da kuma matsalar tsaro, kasar ta ce ta kama wasu mutane 41 da dinbin abubuwan fashewa.

Hukumomi a Sudan, sun ce sun kama wasu mutane 41 dauke da dumbin ababen fashewa.

Babban Atoni janar din kasa, Tagelsir el-Hebre, ya fadawa manema labarai a jiya Larabawa cewa, an samu mutane da ake zargin dauke da ababen fashewar da za su iya yin kaca-kaca da Khartoum, babban birnin kasar.

Kakakin wani sashen jami’an tsaron kasar, Jamar Juma ya ce, wani bincike da aka kaddamar a watan Agustan da ya gabata ne ya kai ga kama ‘yan ta’addan.

A cewarsa, akwai fargabar cewa, ‘yan kasar ta Sudan za su fara kai hare-haren bama-bamai bayan da aka kama wadannan mutane da wadannan dumbin ababen fashewa, wadanda girmansu zai iya haifar da irin fashewar da ta auku a Lebanon a watan da ya gabata.