Gabannin fara ziyarar aiki da shugaba Omar al-Bashir na Sudan, zai kai cadi Laraban nan,Sudan ta kori wasu manyan shugabannin ‘yan tawaye Cadi dake kasar.
Sudan ta fara korar ‘yan tawayen Cadi dake cikin huruminta,gabannin ziyarar aiki da shugaban kasar Sudan din Omar al-Bashir zai kai kasar, yau Laraba. Wan nan ziyara ta Mr. Bashir, ita ce ta farko da zai kai wata kasa wacce take da wakilci a kotun ta Duniya. Kotun ce ta bada sommacin a kama mata shi, bisa zargin laifukkan yaki, da kisan kare dangi. A wani mataki da masu fashin baki suke fassara shi kamar sassauci ne ga Cadi, jami’an Sudan sun ce gwamnatin kasar ta kori gaggan ‘yan tawayen Cadi da dama, ciki har da shugabannin ‘yan tawaye, da suka hada da Mahamat Nouri da Timan Erdimi.