Sudan: An Cinma Yarjejeniya Tsakanin Sojoji Da Farar Hula

An cimma matsaya tsakanin sojoji masu rike da ragamar mulkin kasar Sudan, da tawagar masu neman a maida kasar bisa tafarkin Demokradiyya, yarjejeniyar da aka cimma itace za’a raba mukamai a lokacin mika mulki ga farar hula, don samar da gwamnati mai cin gashin kanta karkashin jagorancin Firai Minista.

A yau Juma’a manzo na musamman a kungiyar hadin kan kasashen Afrika, Mohammed El-Hassan Labat, ya shaidawa manema labarai cewar, bangarorin biyu sun cinma matsaya, don samar da gwamnati hadin kai, wadda za’a dinga karba karba tsakanin sojoji da farar hula na tsawon shekaru 3 ko fiye da haka kadan.

Labat, ya kara da cewar an kuma amince a baiwa sojoji kujeru 5 sai farar hula suma kujeru 5 kana da karin wata kujera 1 ga wani tsohon soja a gwamnatin hadakar.

Sai dai yarjejeniya ta samu nasara ne bayan kwashe kwanaki biyu da aka yi ana tattaunawa mai zafi a birnin Khartoum.

Ana sa ran hakan ya kawo karshen tashin-tashina da aka dade ana yi a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Omar Al-Bashir a watan Afrilu.