Sporting Lisbon Ta Sallami Peseiro

Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon da ke kasar Portugal ta ba da sanarwar sallamar kociyanta Jose Peseiro a ranar Alhamis din da ta gabata.

Hakan ya biyo bayan shan kaye da ta yi ne a hannun kulob din Estoril FC da ci 2 da 1.

Wannan rashin nasarar ta Lisbon a hannun Estoril, karo na hudu kenan a jere a gasar League din kasar.

Shugaban kungiyar Frederico Varandas, shi ya tabbatar da sallamar Peseiro, kuma hakan na zuwa ne duk da kasancewar Sporting a matsayita na 5 a teburin gasar.

Kuma tazarar maki 2 kacal ke tsakaninta da FC Porto wadda ke saman teburin gasar ta bana.

Hakan ya dai kawo karshen Kocin.Peseiro mai shekaru 58 daga Sporting, wanda ya dauki tsawon lokaci har na wa’adi biyu da ya shafe yana horar da kungiyar, inda ya kai ta ga wasan karshe na kofin Europa a shekarar 2005.

Duk da gazawarta a gasar League, Sporting za ta kai zagayen kungiyoyi 16 na gasar Europa, inda ta ke matsayi na biyu a rukuninta na E da tazarar maki 2 tsakaninta da Arsenal da ke saman teburi.

An bayyana sunayen koci kamar su Paulo Sousa tsohon kocin kasar Portugal, da kuma tsohon mai horas da Monaco Leonardo Jardim cikin wadanda ake ganin za'a zaba don maye gurbinsa.