Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta zartas da hukunci mai tsauri akan daya daga cikin manyan shugabanni a fagen wasan kwallon kafa a Afrika.
FIFA ta haramtawa shugaban kwallon kafar na kasar Ghana mai suna Kwesi Nyantakyi, shiga dukkanin al’amuran da suka shafi wasanni har abada.
Bayan haramcin, da aka masa na shiga harkokin wasanni, Mr. Nyantakyi zai kuma biya tarar kudi da ya kai euro dubu 390.
FIFA ta ce daukar matakin ya biyo bayan samun Nyantakyi da laifin cin hanci da rashawa da kuma karya wasu ka’idojinta.
Hukumar ta soma bincikar tsohon shugaban kwallon kafar na Ghana, bayan da Anas Armaya’u Anas, wani dan jarida da ya batar da kama, ya dauki hotonsa a lokacin da yake karbar cin hancin dala dubu 65,000 daga gare shi.
Sai dai tsohon shugaban ya musanta karbar na goron, inda ya ce an hada hoton ne domin bata masa suna.
Wannan dambarwace ta tilastawa Kwesi Nyantakyi sauka daga mukamansa da suka hada da na shugabancin hukumar kwallon kafa ta Ghana, da matsayinsa na mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika (CAF) da kuma barin matsayinsa na dan majalisar koli a
hukumar ta FIFA.
Hukumar FIFA ta ce hukuncin ya shafi dukkan bangarorin wasanni, kama daga matakin kasarsa da kuma matakin kasa da kasa.
Facebook Forum