Har Yanzu Tsohon Mataimakin Shugaban Catalonia Na Tsare

Tsohon Mataimakin Shugaban Catalonia Oriol Junqueras

Kotu a kasar Spain ta yanke hukunci a yau Juma’a kan a ci gaba da tsare Mataimakin Shugaban Catalan Oriol Junqueras, bayan ya kwashe fiye da watanni biyu a gidan yari sakamakon hannu da yake dashi na yunkurin neman yancin kan yankin daga Spain.

A hukuncin nasu , Alkalan sunce akwai hadari cewa shugaban 'yan awaren Junqueras kila ya sake aikata wani laifin idan aka sake shi tunda babu wata shaida da ta nuna yayi watsi da hanyar da yake akai.

An tsare Junqueras ne bisa zargin da ake masa na fandarewa da kuma zuga al’umma tare da amfani da dukiyar al’umma. Hukuncin kotun zai hana shi bayyana a ranar rantsar da sabbin 'yan majalisar Catalan a ranar 7 ga watan Janairu.

Junqueras ya bayyana a gaban kotu ranar Alhamis inda ya bukaci a sake shi don samun damar halartar bikin rantsar da sabbin 'yan majalisun na Catalonia biyo bayan zaben da Spain ta kakaba wanda jam’iyyar 'yan aware sukayi nasarar mafiya yawan kujerun majalisar.