Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka, ta amince da Somaliya a matsayin sabuwar mamba ta takwas a kungiyar a ranar Juma’a, matakin da hukumomi da ‘yan kasuwar kasar suka ce zai bunkasa fannin tattalin arzikin Somaliya.
Kungiyar mai suna EAC a takaice, na dauke da kasashen Burundi, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da Uganda.
An kafa ta ne a shekarar 2010 kuma tana dauke da kusan mutum miliyan 300 daga kasashen kungiyar.
A wani sakon da ya wallafa a Shafin X da ake kira Twitter a da, Ministan yada labarai da al’adun kasar ta Somalia Daud Aweis, ya ce, kasancewar kasar a wannan kungiyar zai budewa Somaliya hanyoyi na ci gaba da kulla kawance.
Shigar kasar ta Somaliya wannan kungiya a yanzu, ya ba ta damar fadada harkokin kasuwancinta tare da samun kusantar karin gabobin teku da tsawonsu ya kai kilomita 3,000 wadanda za su iya bunkasa harkar samun albarkatun man fetur da iskar gas.