Soludo Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Anambra Na Jam'iyyar APGA

  • Murtala Sanyinna

Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya lashe tikitin takarar zaben gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APGA.

Farfesa Charles Soludo ya sami tikitin jam’iyyar ne a zaben da ta gudanar na fidda gwani a Awka babban birnin jihar, inda ya sami kuri’un wakilai 740, daga cikin kuri’u 792 da aka kada.

A yayin da yake bayyana sakamakon zaben na fidda gwani, babban jami’in kula da zaben Samson Olalere, ya ce Soludo ya cika dukan sharuddan dokar zabe da na jam’iyyar ta APGA.

Soludo ya yi nasarar doke abokan takarar sa da suka hada da dan majalisar wakilai Okwudili Ezenwakwo, da Damian Okolo da kuma Thankgod Ibeh.

Jami’in zaben ya ce an yi rijistar wakilai masu zabe 812, inda daga cikin su aka tantance 795, a yayin da kuma 792 ne suka kada kuri’a.

Sakamakon zaben na fidda gwani ya nuna Soludo yana da kuri’u 740, Ezenwakwo 41, Okolo ya sami kuri’u 7, yayin da Ibeh ya ke da kuri’u 4.

Tuni kuma da baturen zaben ya hannunta takardar shaidar zama dan takarar gwamna na jam’iyyar ta APGA ga Soludo.

Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA

Haka kuma gwamnan jihar ta Anambra Willie Obiano wanda shi ma ya shaidi zaben na fidda gwani, ya daga hannun Soludo, domin gabatar da shi a zaman dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ta APGA mai mulkin jihar.

Gwamnan ya taya shi murna, kana ya yi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar da su ba shi goyon baya.

Shi ma dai da yake jawabin amincewa da sakamakon zaben, Soludo ya bayyana farin ciki da ruwan kuri’u da aka yi masa wadanda suka ba shi nasara a zaben.

Haka kuma ya yi alkawarin cewa ba zai ba ‘yan jam’iyyar kunya ba, musamman idan ya sami nasarar lashe zaben gwamnan jihar.

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta tsara za’a gudanar da zaben gwamna a jihar ta Anambra ne a ranar 6 ga watan Nuwamban wannan shekara.