Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Tsaida Ranar Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihohin Ekiti Da Osun


INEC
INEC

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta bayyana ranakun da za’a gudanar da zabukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun, da ke kudancin kasar, a yayin da kuma ta ba da sanarwar kirkiro sababbin rumfunan zabe a fadin kasar.

A lokacin wani taro da hukumar zaben ta gudanar a ofishinta da ke Abuja, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar ta yi matsayar cewa za’a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti a ranar Assabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022, yayin da shi kuma zaben gwamnan jihar Osun zai biyo bayan wata daya, wato ranar Assabar, 18 ga watan Yulin shekarar ta 2022.

Farfesa Yakubu ya ce an ba da sanarwar lokacin gudanar da zabukan ne nan da shekara daya mai zuwa, bisa tsarin da hukumar ta yi na bayyana lokutan zabe da wuri, domin baiwa kowa damar kimtsawa sosai na tunkarar zabe.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)

Haka kuma ya ce hukumar zaben ta soma shirye-shiryen gudanar da sauran zabukan da wa’adin mulkinsu ya kare, a yayin da aka tunkari babban zabe na shekarar 2023.

“Tuni da aka soma aiwatar da jadawalin ayuka da aka tsara na gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra, da kuma zaben majalisun gundumomi na babban birnin tarayya da za’a gudanar a ranar 12 ga watan Fabrairun shekara ta 2022,” in ji shugaban hukumar zaben ta INEC.

Ya kara da cewa haka ma an saka jadawalin ayukan gudanar da zabukan gwamna na jihohin 2 na Ekiti da Osun, a shafin hukumar na yanar gizo, da kuma Kafofin sada zumunta na hukumar.

Akan haka ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ma ‘yan takararsu, da su tabbatar da gudanar da sahihan zabukan fitar da gwani, da kuma gangamin yakin neman zabe cikin tsanaki da kwanciyar hankali.

Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma bayyana sababbin rumfunan zabe har 56,872 da hukumar ta kirkiro, kari akan rumfuna 119,974 da ake da su a fadin kasar tsawon shekaru 25, tun daga shekarar 1996.

Ya bayyana cewa sababbin rumfunan zaben za su soma aiki ne daga zaben gwamnan jihar Anambra da za’a gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG