A cewar wasu mazauna garin Tabbanni lamarin dai ya biyo bayan wani sako da ‘yan bindigar suka bayar a karshen makon da ya gabata, na cewa jama’a su tara musu kudade, umarnin da ‘yan garin suka ‘ki cikawa.
Hakan ya sa ‘yan bindigar suka kai hari inda suka bude wuta kan mai uwa dawabi tare da cinnawa garin wuta, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Kamar yadda wani mazunin garin ya bayyanawa Muryar Amurka, ‘yan bindigar sun kasance barayin Shanu ne dake karbar kudi a wajensu, tare da kwashe musu dabbobi.
Ya zuwa yanzu haka dai babu tabbatacin adadin mutanen da aka kashe, amma wasu alkaluma da ba a tabbatar ba na cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu a wannan hari ya haura 45, ciki har da wani basaraken garin.
Tuni dai jama’ar garin suka fice zuwa wasu garuruwa domin neman mafaka, wadanda kuma suka nufi Sokoto fadar mai alfarma sarkin Musulmi ce ta karbe su.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5