A wani mataki na tsuke bakin aljihu, gwamnatin Jihar Sokoto ta janye dalibanta 39 da ke karatu a jami’o'i daban daban a hadaddiyar Daular Larabawa.
WASHINGTON D.C. —
Za kuma a maida su wasu jami’oi da ke Najeriya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.
Wannan mataki a cewa gwamnatin jihar ta Sokoto na nuni da irin fannonin da gwamnati za ta fi maida hankali a kai.
Akalla Naira miliyan 500 ake kashewa akan daliban su 39, kuma hukumomin jihar sun ce za su kara duba wasu fannonin da gwamnati ke kashe kudade masu dumbin yawa domin a rage ko kuma a soke.
Domin jin karin bayani saurari rahoton wakilinmu Murtal Faruk Sanyinna daga Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5