Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar ‘yan sanda Najeriya tace ta gano makamai da aka boye a ofisoshin wasu jam'iyun siyasa a Sakkwato.
Lamarin zabe a wasu kasashen duniya wasu lokuta yakan zo da yamutsi da tashe-tashen hankula har ma da hasarar rayuka.
Wannan bai rasa nasaba da kokarin da wasu kungiyoyi da hukumomi ke yi na hada ‘yan takara ko jam'iyun siyasa wuri daya su saka hannu ga yarjejeniyar gudanar da lamurra cikin lumana.
Sai dai a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya rundunar ‘yan sanda tace ta kama makamai a ofisoshin wasu jam'iyu da ake tarawa don yin ta'addanci.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Muhammad Usaini Gumel yace sun samu labarin ana tara makaman ne inda suka kai samame suka kama makamai a ofisoshin jam'iyun APC da PDP na karamar hukumar Isa.
Yace makaman sun hada da adduna, sanduna, bindigar gargajiya ta harba ruga da sauran nau'o'in makamai.
To sai dai Muryar Amurka ta tuntubi kakakin jam'iyun da aka kama makaman a ofisoshin su, sun ce ba su da masaniyar haka.
Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce tayi shiri na taimakawa a gudanar da zabe cikin lumana.
Kamar bayani da babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya yayi na cewa sun shirya don taimakawa farar hula wajen samar da kyakkyawan yanayin zabe.
Yace darussan da suka koya wajen kula da tsaro lokutan zabe a jihohin Anambra, Ekiti da Osun su zasu taimaka musu a zabubukan dake tafe.
Tuni jama'ar yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro su ka nuna fargaba abin da kan iya faruwa lokutan zabe.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Tangaza Ibrahim Lawal Ginjo, ya saba kira ga hukumar INEC ta da dauki mutanen tankunan da ke matsalar suyi aiki a yankunan su saboda su suka saba da wuraren.
Da yawa dai na jama'a musamman na yankunan da ke fama da rashin tsaro a Najeriya, ke ta tunanin yadda zabe zai gudana a yankunan su, duba da halin da suka samu kansu a ciki.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5