SOKOTO: Ana Cigaba Da Takaddama Game Da Kafa Masana'antu a Wuraren Da Al'umma Ke Zama

Wata masana'anta a sokoto

An dade ana tada jijiyar wuya a Najeriya kan batun kafa masana'antu a wuraren al'umma, abin da wasu lokuta kan kai ga al'umma daukar mataki ko da mummuna ne kamar abinda ya sha faruwa a yankin Naija Dalta.

Har yanzu ana samun tankiya tsakanin al'ummomi mazauna wuri da kamfanonin da ke sana'a a wurin domin yanzu haka al'ummomi daga kauyuka 15 suna a kotu suna shara'a da kamfanin siminti na BUA da gwamnatin jihar Sakkwato.

An sha ganin yadda ake samun tankiya tsakanin al’umma mazauna wuri ko gwamnati da kamfanonin dake aikin sarrafa kayayyaki a wurin, duk da yake wasu lokuta akan sasanta.

A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya al'ummomi ne daga kauyuka goma sha biyar dake makwabtaka da kanfanin siminti na BUA ke shara'a da kamfanin da kuma gwamnatin jihar Sakkwato akan wasu korafe korafe.

Kotu a Sokoto

Abubakar Kokani Wamakko wakilan jama'ar da ke korafi yace gwamnati tana aune gonakin talakawa ta sayarwa kamfanin BUA ta basu abinda baya isa neman wani gida ko gona, yace dole su dauki mataki kar yaransu su zama hatsabibai saboda rashin gida da gonaki, ko aikin yi.

Fili a Sokoto

Akan hakan suka gurfanar da kamfanin da gwamnatin jihar Sakkwato gaban kotu tun a watan Yuni na wannan shekara.

A zaman da kotun tayi a baya, lauyoyin masu kariya sun nemi kotun ta yi watsi da karar domin bata da hurumin sauraren karar kuma masu shigar da karar basu da hurumin yin karar.

Sai dai a zaman kotun na hukunci akan wannan bukatar mai shara'a Kabiru Ibrahim Ahmad yace kotun da masu shigar da karar suna da hurumin yin karar.

Lauyan masu shigar da kara Mustapha Na'abu wanda bai yarda a nada sautinsa ba yace sun yi farin ciki da wannan hukuncin na kotu.

Shi kuwa lauyan kamfanin na BUA Abdulrahman Isa Wasagu cewa yayi bai kamata kotu ta saurari karar ba saboda akwai wasu abubuwa da masu shigar da kara ya kamata su yi kuma basu yi ba, amma dai zasu karbi kofin hukuncin su yi nazari da shawarar abinda ya kamata.

Muryar Amurka ta nema ta jin ta bakin lauyan gwamnatin jihar, Barrister Bello Musa sai dai yace baya da iznin yin magana da manema labarai.

Duk da kasancewa ana kotu, al’ummomi da abin ya shafa suna ci gaba da kokawa.

Tun kafin wannan lokacin kamfanin na siminti ya jima yana bayar da tallafi ga al'ummomi da yake makwabtaka da su, na bayan nan shine aikin samar da ruwa da na'urar rarraba harken wutar lantarki ga jama'ar Gagi da Gidan Baduwa.

Yanzu dai babbar kotun mai daraja ta uku ta Sakkwato ta saka ranar 12 ga Decemba domin sake karanta karar. Yayinda al'ummomin suka ce sun shirya tsaf doman neman abinda suke bukata.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO: Ana Cigaba Gwaggamayar Game Da Kafa Masana'antu a Wuraren Da Al'umma Ke Zama